Gwamnatin Jigawa ta yaba da tsarin FMBN na tallafa wa ma’aikata mallakar gidaje

Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da tsarin da Bankin Ba da Lamunin Gidaje na Ƙasa, FMBN, ya bullo da shi domin taimaka wa ma’aikatan jihar wajen mallakar gidaje.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai na yini guda kan yadda ake bayar da kaso 2.5 cikin 100 na albashin ma’aikata zuwa Asusun Gidaje na Ƙasa.
An gudanar da taron ne tare da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago na jihar.
Alhaji Dagaceri ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin FMBN da gwamnatin jihar na taimakawa wajen samar da hanyoyin da ma’aikata za su samu damar mallakar gidaje cikin sauƙi.
Ya ce gwamnatin jihar na maraba da duk wani shiri da zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin gidaje da ma’aikata ke fuskanta.
Da yake bayyana manufar taron, Shugaban FMBN na Jihar Jigawa, Abdullahi Adamu Gidare, ya ce bankin ya shirya taron ne domin wayar da kan ma’aikata kan yadda Asusun Gidaje na Ƙasa ke aiki da kuma hanyoyin da za su bi domin cin gajiyar shirin.
Ya ce taron zai taimaka wajen ƙara wa ma’aikata fahimta kan tsarin da kuma yadda za su iya amfani da shi wajen samun damar mallakar gidaje.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, reshen Jihar Jigawa, wanda Ma’ajin ƙungiyar, Abdulkadir Yunusa, ya wakilta, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga shirin.
Ya ce NLC za ta ci gaba da wayar da kan ma’aikata kan tsarin Asusun Gidaje na Ƙasa da kuma yadda za su amfana da shi.
Bankin Ba da Lamunin Gidaje na Ƙasa, FMBN, ya shafe shekaru yana aiwatar da shirye-shiryen samar da gidaje ga ‘yan Najeriya, da nufin sauƙaƙa musu damar mallakar gidaje.



