Koma Labarai
Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta sha alwashin tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnatin jihar ke warewa domin samar da ruwan sha sun haifar da sakamakon da ya dace,

Usman Muhammad Ismail 0 views
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta sha alwashin tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnatin jihar ke warewa domin samar da ruwan sha sun haifar da sakamakon da ya dace,

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta sha alwashin tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnatin jihar ke warewa domin samar da ruwan sha sun haifar da sakamakon da ya dace, ta hanyar sa ido kan ayyukan da ake gudanarwa a wannan fanni.

Mukaddashin shugaban kwamitin musamman na Majalisar da ke rangadin duba ayyukan samar da ruwan sha a shiyyar Jigawa ta Arewa maso Yamma, Hon. Yusuf Soja Bulangu, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai cibiyoyin samar da ruwan sha da gwamnatin jihar ta gina domin amfanin al'umma a yankin Masarautar Ringim.

Hon. Yusuf Soja Bulangu, wanda ke wakiltar mazabar Bulangu, ya ce rangadin zai taimaka wa Majalisar wajen tantance yadda aka aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, musamman a fannin samar da tsaftataccen ruwan sha.

Ya ƙara da cewa wannan mataki na da muhimmanci duba da yadda Majalisar ke shirin karɓar baƙuncin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 mai zuwa.

A yayin rangadin, Hon. Yusuf Soja Bulangu ya samu rakiyar Hon. Masaud Muhammad Naruwa, wanda ke wakiltar mazabar Babura.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar wa zauren Majalisar rahoton abubuwan da ya gani da kuma halin da ayyukan samar da ruwan sha ke ciki bayan kammala rangadin.

Wannan rangadi na daga cikin matakan da Majalisar ke ɗauka domin ƙarfafa sa ido kan ayyukan gwamnati da tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake warewa domin jin daɗin al'umma sun cimma manufar da aka tsara musu.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM