Koma Labarai
Labarai

Za mu kawar da talauci a Najeriya, amma hakan zai ɗauki lokaci - Tinubu

Usman Muhammad Ismail 0 views
Za mu kawar da talauci a Najeriya, amma hakan zai ɗauki lokaci - Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta yi nasarar kawar da talauci a ƙasar, sai dai hakan zai ɗauki lokaci.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar wa ‘yan Najeriya ranar Alhamis domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Ya ce kawar da talauci na buƙatar jajircewa, ci gaba mai ɗorewa da samar da miliyoyin guraben ayyukan yi masu amfani.

Shugaban ya ce gwamnatin sa ta ɗauki matakai masu tsauri wajen gyara tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa gyare-gyaren da aka fara sun aza tubalin samun ci gaba da wadata.

A cewarsa, Najeriya ta gyara tafiyar tattalin arzikinta, kuma yanzu lokaci ya yi da ‘yan ƙasar za su ci gaba da gina makomar ƙasar ba tare da waiwaya baya ba.

Ya ce babban burin gwamnatin shi ne gina Najeriya mai yalwa da dama ga kowa, inda za a raba arziki yadda ya kamata, tare da bai wa kowane yaro damar cimma burinsa ba tare da la’akari da yanayin da aka haife shi ba.

Shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu haƙuri da haɗin kai domin ganin an cimma wannan buri.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM