Kamfanin Jirgin Rano Air zai fara zirga- zirga tsakanin Dutse da Abuja bayan sanya hanu kan yarjejeniya da gwamnatin jihar X Jigawa.

An cimma matsayar fara zirga-zirgar ne a ya yin Majalisar Zartarwa jihar na wannan mako karkashin jagorancin gwamna Malam Umar Namadi wadda ke gudana a gidan gwamnatin jihar Jigawa dake Dutse.
Tini gwamnatin jihar da kuma kamfanin Jirgin na Rano Air suka sanya hanu kan wata yarjejeniyar fara Jigilar nan da dan lokaci kadan, daga Abuja zuwa Dutse da kuma Dutse zuwa Abuja, da nufin saukakawa 'yan kasuwa da matafiya da kuma ma'aikata da kuma bunkasa tattalin arziki.
A cewar kwamishinan yada Labaran jihar Alhaji Sagiru Musa Ahmad a'na sa ran fara zirga-zirgar zai ƙara jawo masu zuba jari da haɓaka harkokin yawon buɗe ido da tabbatar da cikakken amfani da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa dake Dutse da kuma samar da sabbin guraben ayyukan yi ga al'ummar jihar musamman matasa.
Kazalika a zaman majalisar ta amince da kafa kwamatin tsara yadda lamarin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Injiniya Aminu Usman Gumel.



