Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce alwashin ci gaba daukar matakan magance matsalar zaizayar ƙasa dake damun sassan jihar daban-daban.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce alwashin ci gaba daukar matakan magance matsalar zaizayar ƙasa dake damun sassan jihar daban-daban.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar duba aiyukan da gwamnatinsa ke aiwatar a yankin karamar hukumar ciki harda aikin zaizayar kasa a garin Kila da aka bada aikinsa kan Naira biliyan 2 da miliyan 600.

Duk da kasancewar gwamnan ya nuna gamsuwa da yadda aikin ke gudana, sai dai ya umarci kamfanin da ya ƙara kara yawan kayan aikin manyan magudanan ruwan da suka hada da Duwatsu da Karfe da kara ingancinsa, wadda hakan tasa gwamna kara adadin kudin aikin zuwa Naira biliyan 3 daga Naira miliyan 2 da miliyan 600 da aka bayar da aikin tun da farko.

Kazalika gwamna Malam Umar Namadi ya ce zaizayar ƙasa ta daɗe tana barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar garin Kila, wadda hakan tasa gwamnatinsa ta ɗauki matakin kawo ƙarshen wannan matsalar da samarwa da mutane nutsuwa da kwamciyar hankali.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa domin dakile matsalolin zaizayar kasar dake yin barazana ga walwalar al'ummar jihar ya fara tattaunawa da Ofishin aiyukan Muhalli na tarayya domin samun ƙarin haɗin gwiwa wajen aiwatar da ayyukan magance matsalar, kamar yadda aka magance hakan a Unguwar Kargo da Danmasara dake Birnin Dutse.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM