Koma Labarai
Labarai

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin CN Hassan Katangana Kabaju ta lashe Award of Excellence a fannin magani da gyaran masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin CN Hassan Katangana Kabaju ta lashe Award of Excellence a fannin magani da gyaran masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Hukumar NDLEA reshen Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin CN Hassan Katangana Kabaju ta lashe Award of Excellence kan fannin Magani da Gyaran Masu Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi.

Shugaban NDLEA na ƙasa, Brig. Gen. Buba Marwa (Rtd) ne ya ba da lambar yabon a ranar 13 ga Agusta, 2026, saboda gagarumin aikin da rundunar ke yi wajen dawo da rayuwar masu fama da shaye-shaye.

Kwamandan ya gode wa jami'an rundunar tare da yabawa Gwamna Malam Umar Namadi Danmodi bisa tallafin da ya bayar wajen samar da cibiyar gyaran hali da kuma ci gaba da tallafa wa ayyukanta.

NDLEA Jigawa – Ba wai yaƙi da miyagun kwayoyi kaɗai ba, har ma da dawo da rayuka.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM