Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya kaddamar sanya hanu kan dokar wayar da kan matasa illar ta'ammali da kayan maye da kuma canja halayya.
Usman Muhammad Ismail 0 views

Namadi ya ce tun lokacin da ya karbi rantsuwa a shekarar 2023 ya yi alkawarin tallafawa aiyukan hukumomin tsaro da kuma daukar matakan dakile matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Kazalika ya bukaci kwamatocin kattakwana da aka kafa don aiwatar da dokokin dasu kasance masu aiki tukuru, kamar yadda aka zabosu bisa cancanta.
Gwamna Namadi ya kara da cewa a'na iya kawo karshen ta'ammali da kayan maye matukar dukkan masu ruwa da tsaki da sauran al'umma zasu yi aikinsu yadda ya kamata.



