Gwamnatin Kano za ta samar da rijiyoyin burtsatse a dukkan mazaɓu 484 na jihar

Gwamnatin Kano ta yi alƙawarin samar da rijiyoyin burtsatse a dukkan mazabu 484 da ke faɗin jihar domin inganta rayuwar al’ummomin karkara.
Kwamishinan Ma’aikatar raya karkara da ci gaban al’umma, Dr Abdulkadir Abdussalam ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron horaswa na kwanaki biyu kan tsarawa da aiwatar da tsarin bunƙasa karkara mai ɗorewa na shekaru 5 daga shekarar 2026 zuwa 2030.
Dr Abdussalam ya ce gwamnatin Gwamna Abba ta kashe kuɗaɗe masu yawa a bara, lamarin da ya bai wa ma’aikatar sa damar zagaya ƙananan hukumomi 44 na jihar tare da gudanar da tarukan jin ra’ayin al’umma domin tsara manufar bunƙasa karkarar cikin shekaru 5 masu zuwa.
Ya ce gwamnatin Kano ta kuduri aniyar magance ƙalubalen da ke addabar yankunan karkara a cikin shekaru biyar masu zuwa ta hanyar aiwatar da ayyukan raya ƙasa da inganta walwalar al’umma.
A nasa jawabin, ɗan majalisar dokokin Kano mai wakiltar Doguwa kuma mamba a kwamitin raya karkara, Alhaji Salisu Ibrahim Doguwa, ya yabawa gwamnatin jihar da ma’aikatar raya karkara bisa ƙaddamar da tsarin wanda ya ce ci gaba ne me ɗorewa.


