Koma Labarai
Labarai

Babbar Kotun tarayya mai zamanta a nan Dutse ta Kori karar da Alhaji Ishaq El Yakub Nabayi ya shiga

Usman Muhammad Ismail 0 views
Babbar Kotun tarayya mai zamanta a nan Dutse ta Kori karar da Alhaji Ishaq El Yakub Nabayi ya shiga

Babbar Kotun tarayya mai zamanta a nan Dutse ta Kori karar da Alhaji Ishaq El Yakub Nabayi ya shigar kan zaben fitar da gwanin dan takarar kujerar wakilcin Hadeja da Auyo da Kafin-Hausa a inuwar Jamiyar APC tare da umartarsa ya biya Naira miliyan 1 da dubu 500 ga wadan da ya yi karar kan bata musu lokaci.

Da yake yanke hukunci alkalin Kotun mai shari'a Ibrahim Muhammad Buba yace mai kara ya kasa gabatarwa da Kotun gamsassun hujjoji kan zaben fitar da gwanin da Aliyu Hussaini Jabo ya samu nasara, wadda a sabo da haka ne ma ya Umarci shi ya jamiyar APC da hukumar zabe da kuma dan takarar Naira dubu dari biyar ga kowane a matsayin diyyar bata musu lokaci.

Barr Baffa Alhassan shi ne lauyan jamiyar APC a wannan shari'a kuma ya yiwa Freedom Radio karin haske kan yadda hukuncin ya kasance.

Game da Labaran da cewa tini mai karar ya janye kararsa kafin yanke hukunci, Barr Baffa yace ba'a janye kara a kafafan sada zumunta don haka Kotu batasan da wannan labari ba, kuma ta Riga ta zatar da hukuncin da ya dace.

Mun yi kokarin jin hanzarin lauyan mai kara ko wadda ya yi karar amma hakan bai yiwuba kasancewar babu wadda ya halarci zaman Kotun daga ciki.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM