Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar jigawa ta yi kira ga masu kemis-kemis da su kaucewa safarar miyagun kwayoyi.
Usman Muhammad Ismail 0 views

Kwamandan hukumar anan jihar Jigawa Hassan Kabejo katangana ne yayi wannan Kiran, yayin taron karawa juna sani kan illolin da safarar miyagun kwayoyi ke haifarwa a kasa. Wanda kungiyar masu sayar da magungunan kemis hadin gwiwa da NDLEA suka gudanar a kwalejin kimiyya da fasaha dake nan Dutse.



