NAFDAC TA ƘARA ZAGE DAMTSE WAJEN WAYAR DA KAI KAN MUHIMMANCIN BA DA NONON UWA ZALLA A JIHAR JIGAWA

Wakiliyar NAFDAC a Jihar Jigawa, Samira Hamza, tare da jami'an Hukumar Lafiya ta jihar Jigawa, sun bayyana hakan ne a wata hira da suka yi a Freedom Radio, a wani bangare na Makon Wayar da Kai Kan Ba da Nonon Uwa Zalla, wanda ake gudanarwa daga 1 zuwa 7 ga Agusta, 2026.
Sun bayyana cewa nonon uwa zalla na tsawon watanni shida na farko yana da matuƙar muhimmanci wajen gina garkuwar jikin jarirai, rage kamuwa da cututtuka, inganta girma da ƙwaƙwalwa, tare da taimakawa uwa wajen samun lafiya bayan haihuwa.
Samira Hamza ta yi kira ga iyaye mata da kada su yi amfani da ruwa, wasu abubuwan sha ko abinci ga jarirai kafin cikar watanni shida, domin nonon uwa kaɗai ya wadatar da jariri da dukkan sinadarai da yake buƙata a wannan lokaci.
Ta kuma buƙaci shugabannin al'umma, malamai, kafafen yaɗa labarai da ma'aikatan lafiya su ci gaba da wayar da kan jama'a, domin tabbatar da cewa kowane jariri ya samu damar fara rayuwa cikin ƙoshin lafiya.
A ƙarshe, NAFDAC da Hukumar Lafiya sun jaddada cewa kare lafiyar jariri yana farawa ne da ba shi nonon uwa zalla, tare da yin kira ga al'umma su mara wa wannan gangami baya domin samar da al'umma mai ƙoshin lafiya da ingantacciyar makoma.
