Koma Labarai
Lafiya

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa, NAFDAC, ta gudanar da wani shirin wayar da kan jama’a a Makaranta kimiya da fasaha da ke Dutse,

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa, NAFDAC, ta gudanar da wani shirin wayar da kan jama’a a Makaranta kimiya da fasaha da ke  Dutse,

Shirin ya mayar da hankali ne wajen wayar da kan ɗalibai, ma’aikata da sauran al’ummar makarantar kan muhimman dokoki da ka’idojin da suka shafi ingancin abinci, ƙara sinadaran gina jiki cikin abinci, hana gurɓata ko sauya ingancin abinci, da kuma lasisin kayayyaki da wuraren samar da abinci.

A yayin shirin, mahalarta sun samu ƙarin bayani kan muhimmancin bin ƙa’idojin NAFDAC domin tabbatar da cewa abincin da ake samarwa da sayarwa yana da lafiya, inganci, kuma an yi masa cikakken lakabi kamar yadda doka ta tanada.

Hukumar ta kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin NAFDAC, shugabancin makarantar, ɗalibai da masu sayar da abinci a cikin makarantar da kewayenta, domin kare lafiyar jama’a.

A ƙarshe, an buƙaci mahalarta da su zama jakadu wajen wayar da kan al’umma game da amincin abinci, tare da tallafa wa ƙoƙarin NAFDAC na tabbatar da cewa jama’a suna amfani da abinci mai tsafta, lafiya da inganci.

Shirin ya samu karɓuwa daga mahalarta, inda suka bayyana jin daɗinsu tare da nuna cewa sun ƙara samun ilimi mai amfani game da ka’idojin abinci, food fortification, hana gurɓatar abinci da kuma bin ƙa’idojin lasisi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM