Wani bincike ya nuna cewa kimanin mutane 19,638 ne ke fama da makantar idanu biyu a jihar jigawa,

yayin da 27,026 ke fama da makanta a ido guda.
An bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon binciken Rapid Assessment of Avoidable Blindness (RAAB7) da aka gudanar a nan birnin Dutse.
Haka kuma, binciken ya nuna cewa kimanin mutane 36,623 na bukatar a yi musu tiyatar Katarak.
Bincike ya kuma gano cewa cutar Katarak ita ce babbar sanadin makanta a Jihar Jigawa, inda take da kashi 40.8 cikin 100 na dukkan lamuran makanta a jihar.
Kwararren likitan ido, Dr. Tafida Abubakar, ya ce Glaucoma ce ta biyu wajen haddasa makanta, da kashi 23.6 cikin 100, yayin da Trachoma da raunukan ido suka kai kashi 21.1 cikin 100.
Da yake magana kan matakan da suka dace, Dr. Tafida Abubakar ya ce akwai bukatar a kara saukaka samun tiyatar Katarak tare da kara wayar da kan jama'a domin su rika zuwa asibitocin ido da wuri.

