Freedom Radio Dutse
Muryar Jama'a, Dutse
← Labarai
Siyasa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware maƙudan kuɗaɗe domin gyara da gina masallatan Juma'a da na unguwanni

JG/TENDER

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware maƙudan kuɗaɗe domin gyara da gina masallatan Juma'a da na unguwanni, tare da kewaye makabartu a mazabu 30 na 'yan Majalisar Dokokin Jihar.

Babban Sakataren Kuɗi da Mulki na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Sa'idu, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron karɓar tayin kwangilar ayyukan a Dutse.

Freedom Radio Dutse 99.5 FM
Freedom Radio Dutse 99.5 FM · Kai tsaye
Live