Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi maraba da wasu magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC
Aisha Hudu 0 views

Atiku ya bayyana cewa waɗanda suka kafa gida suka fice daga cikinsa, ya kamata 'yan Najeriya su tambayi dalilin hakan, yana mai cewa sun gaji da yunwa da rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas Ɗan takarar shugaban ƙasar na ADC ya ce yana fatan karɓar waɗanda suka sauya sheƙar a hukumance, tare da yin alƙawarin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da tsadar rayuwa idan suka samu nasara.



