Koma Labarai
Tsaro

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargi da mallakar bindiga ƙirar gida ba bisa ƙa’ida ba, harsasai da wasu kayayyaki masu alaƙa da aikata laifuka.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargi da mallakar bindiga ƙirar gida ba bisa ƙa’ida ba, harsasai da wasu kayayyaki masu alaƙa da aikata laifuka.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar a yau Talata, 20 ga Oktoba, 2026, ya ce jami’an Operation Salama ne suka kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, a kan hanyar Nguru zuwa Birniwa.

Sanarwar ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin a matsayin Bello Juli, mai shekara 22; Abdullahi Yakubu, mai shekara 30; da Bashir Mohd, mai shekara 25. Dukkansu mazauna ƙauyen Kyarana ne da ke ƙaramar hukumar Kiru ta jihar Kano.

Kayayyakin da aka samu a hannunsu sun haɗa da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsasai ƙirar gida guda uku, adduna, baka da kibiyoyi, da kuma barkonon tsohuwa.

Rundunar ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar, SCID, da ke Dutse.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa taka-tsantsan da jajircewarsu. Ya kuma umarci jami’an rundunar da su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri tare da ƙara yawan sintiri a faɗin jihar.

Haka kuma, kwamishinan ya buƙaci al’umma da su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani motsi ko aiki da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da tsaro ga mazauna jihar da baƙi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM