Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ta fara bincike kan rasuwar wani mutum mai shekaru 60 da ya rasu a wani otal da ke Dutse bayan ya shiga tare da wata budurwa mai shekaru 20.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ta fara bincike kan mutuwar ba-zata da aka samu a wani otal da ke cikin birnin Dutse, yana yin da zama akwai zargi.
A ranar Talatar nan 21 ga Yuli wannan shekara ta 2026 namacin, mai shekaru 60, ya shiga otal ɗin tare da wata budurwa mai shekaru 20, kuma bayan ya nemi a kawo masa abinci sai ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi.
Wannan dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar SP Shi'isu Lawan Adam ya fitar, wadda ya ce da samun rahoton faruwar abin ne Rundunar ta tura jami'anta dake Unguwar gurin da abin ya faru, inda cikin gaggawa suka garzayawa da mutumin zuwa babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa bayan yan gwaje-gwaje.
Tini dai Jami'an dake bincike suka killace wurin da abin ya faru tare da gudanar da bincike kan abinci da abubuwan sha, ciki harda wani sinadari da ake zargin na ƙara ƙarfin jima'i ne, da wasu kayayyakin marigayin domin ci gaba da bincike.
A cewar Rundunar bayan an kammala duk matakan da suka dace, an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana'iza bisa ga buƙatarsu, ya yin da Budurwar da ke tare da shi a lokacin da ya faru ke ci gaba da baiwa jami'an dake bincike haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen aikin da suke.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Jigawa ya tabbatar wa al'umma cewa binciken zai gudana cikin adalci da ƙwarewa, tare da kira ga jama'a da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
