Koma Labarai
Tsaro

Hukumomin Nijar sun tabbatar da tsare ɗan jarida Moussa Kaka

Usman Muhammad Ismail 0 views
Hukumomin Nijar sun tabbatar da tsare ɗan jarida Moussa Kaka

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa fitaccen dan jarida Moussa Kaka yana raye kuma yana hannun gwamnati, fiye da wata guda bayan bacewarsa a Yamai, babban birnin kasar.

Kaka, mai shekara 66, wanda shi ne babban daraktan gidan talabijin da rediyo na Saraounia kuma tsohon wakilin gidan rediyon RFI, ya bace ne a ranar 31 ga Agusta bayan ya bar ofishinsa domin komawa gida.

Ministan shari'a da kare hakkin bil'adama na Nijar, Alio Daouda, ya shaida wa kungiyar Reporters Without Borders (RSF) cewa ana zargin Kaka da aikata wani laifi kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu. Sai dai bai bayyana inda ake tsare da shi ko kuma irin laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.

RSF ta ce rashin bayyana halin da Kaka yake ciki tsawon fiye da wata guda ya yi daidai da abin da ake kira batar da mutum ta hanyar amfani da ƙarfi inda kuma kungiyar ta buƙaci a sake shi.

Lamarin Kaka na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun koma baya a 'yancin aikin jarida a kasashe mambobin AES tun bayan da gwamnatocin soja suka karbi iko a kasashen uku na Nijar da Mali da Burkina Faso.

A cewar Rahoton na RSF kan ƴancin ƴan jarida na 2026, Burkina Faso tana matsayi na 110, Nijar na 120, yayin da Mali ke matsayi na 121. RSF ta ce hukumomin soji a kasashen AES na kara amfani da dokokin tsaron kasa da na laifukan intanet wajen daukar mataki kan 'yan jarida.

Kungiyar ta ce akalla 'yan jarida biyar na tsare a Nijar, daya a Mali, yayin da wasu 'yan jaridar Burkina Faso biyu, Serge Oulon da Moussa Sareba, har yanzu ba a san inda suke ba.

Dan jarida mai binciken ƙwaƙwaf Atiana Serge Oulon ya bace tun bayan sace shi a shekarar 2024. Wani bincike da aka gudanar a 2026 ya ce jami’na tsaro sun tsare shi a asirce tare da azabtar da shi.

'Yancin aikin jarida ya tabarbare matuka a kasashen AES. A Mali, an kama dan jarida Youssouf Sissoko, daga bisani kuma aka yanke masa hukunci bayan ya wallafa kalaman sukar shugaban mulkin sojin Nijar.

A kasashen uku, an rufe ko takaita ayyukan wasu kafafen yada labarai, tare da kama 'yan jarida. A Burkina Faso kuma, kungiyoyin kare 'yancin 'yan jarida da suka hada da CPJ, RSF, IFJ da Human Rights Watch sun ce an tilasta wa wasu 'yan jaridar da ke sukar hukumomi.

A yayin da ake ci gaba da wannan matsin lamba, batun Kaka yana da muhimmanci ba wai kawai saboda shahararsa ba, har ma yana kara haifar da tambayoyi game da makomar 'yancin aikin jarida a tsakanin kasashen AES, wadanda ke kara hada kai da juna.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM