ICPC ta binciki gidan Nasir El-Rufa'i da ke Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa, ICPC, sun binciki gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, da ke Abuja a ranar Alhamis 19 ga watan Fabrairu, 2026.
Wannan na cikin sanarwar da mai bai wa tsohon gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce, jami’an hukumar sun isa gidan El-Rufa'i, a ranar Alhamis, inda nan take suka fara binciken dukkan sassan gidan.
Kazalika, Lauyan El-Rufa'i, Ubong Akpan, ya yi Allah wadai da matakin, yana mai cewa "binciken da jami'an suka yi ba bisa ƙa’ida ba ne kuma ya saba wa dokoki da haƙƙoƙin ɗan Adam.”
Rahotanni sun bayyana cewa, tun a ranar Laraba 18 ga Fabrairu, 2026, hukumar ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannunta dangane da wani bincike da ta ke yi a kansa.
Sai dai Hukumar ba ta bayar da cikakken bayani kan irin binciken da ake yi a kan Nasir El-Rura'i, ba.
