Koma Labarai
Labarai

NOA ta gargaɗi ƴan kasuwa kan ta'adar sanyawa kayan abinci magani da ƙara masa kuɗi da gangan

Muhammad Aminu Umar Shuwajo 6 views

Hukumar wayar da kan mutane ta kasa NOA ta gargadi yan kasuwa a kasar nan kan ta'adar sanyawa kayan abinci magani tare da kara masa kudi da gangan musamman a lokacin Ibadar Azumi.

Babban daraktan hukumar Malam Issa-Onilu ne ya yi wannan gargadi bayan samun wani rahoto game da wasu yan kasuwar dake sanya kayan abinci magani suna boyewa don cin kazamar riba a irin wannan lokaci na Ibadah.

A cewar Issa irin wannan dabi'a ba kawai tattalin arziki take ruguzawa ba ta sabawa ka ida musamman ma a wannan lokaci da ake bukatar sadaukarwa da taimakon juna da nuna tausayi.

Haka nan babban daraktan ya bayyana ta'adar a matsayin wadda ke cutar da al'ummar kasar nan musamman marassa da talakawa, harma ya bukaci yan kasuwa dasu kasance masu jin tsoron Allah da tausayi.

Sai dai ya ce hukumar ta NOA za ta ci gaba da bibiyar lamarin tare da sanya masu ruwa da tsaki cikin lamarin domin samar da walwalar al'umma da al'adu don tabbatar da hadin kan kasar.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM