IMF zai baiwa ƙasar burkina faso tallafin kusan dala miliyan 34
Asusun ba da Lamuni na duniya IMF, ya amince ya bai wa Burkina Faso dala miliyan 332, take yanke a matsayin zango na hudu na wani bangare na shirin ba da agaji ga kasar da ke yammacin Afirka.
Wannan sabon kaso na nuna cewa jimillar kudaden da Burkina Faso ta samu daga Asusun na IMF a matsayin agaji sun tashi a dala miliyan 165,8 kamar yadda sanarwar hukumar ta nunar.
A daura da wannan tallafi, Asusun IMF ya kuma sahale bai wa Burkina Faso rancen dala miliyan 124.3 da za ta biya a cikin dogon lokaci a karakashin wani shiri na yaki da dumamar yanayi mai lakabi da 'RSF'.
A watan Satumban 2023 ne dai Asusun IMF, ya amince da wani shiri na ba wa Burkina Faso tallafin dala miliyan 305 domin karfafa wa hukumomin kasar gwiwa wajen yakar talauci a tsakanin al'umma.
