Koma Labarai
Ilimi

Kimanin dalibai 3,445 ne za su rubuta jarabawar shiga makarantun firamare na kwana da kananan makarantun sakandiren kimiyya da ke fadin Jihar Jigawa.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Kimanin dalibai 3,445 ne za su rubuta jarabawar shiga makarantun firamare na kwana da kananan makarantun sakandiren kimiyya da ke fadin Jihar Jigawa.

Shugaban Hukumar Ilimin Matakin Farko ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana hakan ta bakin Daraktan Kudi da Mulki na hukumar, Alhaji Bello Madaki, yayin da ya ziyarci daya daga cikin cibiyoyin da ake gudanar da jarabawar da ke garin Bulangu.

Alhaji Bello Madaki ya ce an tanadi cibiyoyi bakwai domin gudanar da jarabawar, da nufin rage wa iyaye wahalar jigilar 'ya'yansu zuwa wuraren rubuta jarabawar.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta tura jami'anta zuwa cibiyoyin jarabawar domin sa ido da tabbatar da cewa an gudanar da jarabawar cikin tsari, gaskiya da adalci.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM