Koma Labarai
Shari'a

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta sanya ranar 5 ga Oktoba, 2026, domin yanke shawara kan ko tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan Malam Lawan Triumph.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta sanya ranar 5 ga Oktoba, 2026, domin yanke shawara kan ko tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan Malam Lawan Triumph.

Wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma ya ruwaito cewa, a zaman da Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya jagoranta, lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Haji, da lauyan waɗanda ake ƙara, Barista Abdurrazak Ahmad, sun gabatar da hujjoji kan batun hurumin kotun.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, alƙalin ya ce ya fahimci buƙatunsu, kuma zai gudanar da shari’ar bisa tsari. Daga nan ya ɗage zaman zuwa ranar 5 ga Oktoba domin bayyana shawarar kotun kan hurumin sauraron ƙarar.

Tunda fari dai wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci ne suka shigar da ƙarar kan Malam Lawan Triumph, bisa zargin batanci da yunƙurin tada tarzoma. Kotun ba ta yanke hukunci kan waɗannan zarge-zarge ba.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM