Wata Kotun tarayya dake Abuja ta dage ci gaba da saurarar shari'ar EFCC da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido kan zarge-zarge 37.

Hukumar Yaƙi da masu yiwa tattalin arziki zagom kasa EFCC ta ci gaba da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Dakta Sule Lamido, da 'ya'yansa a gaban wata Kotun tarayya kan zarge-zarge 37.
Laifukan da ake zargin tsohon gwamnan sun hada da cin hanci bayar da Kwangilar bogi ta Kudaden da suka kai Naira biliyan 1.35.
A cewar EFCC wadan da ake tuhuma sun aikata waɗan nan laifuffuka ne a lokacin da tsohon gwamnan ke mulkin jihar Jigawa tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015.
A zaman kotun na ranar Litinin din nan lauyan hukumar EFCC, Chile Okoroma (SAN), ya sanar da kotun cewa l, babban lauyan waɗan da ake tuhuma ya aikewa da kotun wasiƙar cewa ba zai samu halartar zaman ba sabo da yana yin rashin lafiya harma an yi masa tiyata wadda ya nemi a ɗage shari'ar.
Sai dai lauyan EFCC ya yi masa fatan samun lafiya cikin gaggawa, amma ya ce ya dace a samu wani daga cikin lauyoyin tawagarsa ya wakilce shi domin kada shari'ar ta ƙara samun tsaiko irin wadda ta fukanta a baya.
Bayan haka ya tunawa kotun cewa an fara wannan shari'ar ne tun a shekarar 2015, inda ya jaddada buƙatar dake akwai na kaucewa jinkirin yin shari'ar irin na baya.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, mai Shari'a Ojukwu ta amince da buƙatar EFCC na ɗage ci gaba saurarar shari'ar zuwa Gobe Talata 21 ga wannan wata Yuli, 2026, a matsayin ranar ci gaba da sauraron shari'ar.
