Koma Labarai
Iftila'i

Ana ci gaba da aikin neman waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a garin Malamawar Yandutse, da ke ƙaramar hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Ana ci gaba da aikin neman waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a garin Malamawar Yandutse, da ke ƙaramar hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Ana ci gaba da aikin neman waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a garin Malamawar Yandutse, da ke ƙaramar hukumar Ringim a Jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu an ceto mutane 16, yayin da mutane shida suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin.

Wasu daga cikin shaidun gani da ido sun shaida wa Freedom Radio cewa har yanzu jami'an ceto da mazauna yankin na ci gaba da aikin bincike da ceto a wurin da lamarin ya faru.

A halin da ake ciki kuma, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya halarci jana'izar tare da yin sallar jana'iza ga mutane biyar daga cikin shida da suka rasa rayukansu.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse99.5 FM