Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware maƙudan kuɗaɗe domin gyara da gina masallatan Juma'a da na unguwanni
Usman Muhammad Ismail 0 views

JG/TENDER
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware maƙudan kuɗaɗe domin gyara da gina masallatan Juma'a da na unguwanni, tare da kewaye makabartu a mazabu 30 na 'yan Majalisar Dokokin Jihar.
Babban Sakataren Kuɗi da Mulki na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Sa'idu, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron karɓar tayin kwangilar ayyukan a Dutse.
