Koma Labarai
Tattalin Arziki

Tashar CNG ta farko a Dutsen jihar Jigawa ta fara aiki.

Usman Muhammad Ismail 0 views
Tashar CNG ta farko a Dutsen jihar Jigawa ta fara aiki.

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara amfani da tashar CNG ta farko a jihar, wadda ke birnin Dutse.

Tashar za ta bai wa masu motoci damar amfani da CNG a madadin fetur, tare da ba da damar sauya wasu motocin fetur zuwa CNG.

Ana sa ran matakin zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da dogaro da man fetur, tare da samar da sabbin ayyukan yi ga masu sana’ar gyaran motoci da sauya motocin zuwa CNG.

Gwamnatin jihar ta ce wannan na daga cikin shirye-shiryenta na amfani da sabbin hanyoyin makamashi domin rage wa jama’a nauyin tsadar rayuwa.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM