Koma Labarai
Zamantakewa

An ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi miliyan ɗaya a yankin Arewacin Najeriya da nufin yaƙi da sauyin yanayi da kuma kare muhalli.

Usman Muhammad Ismail 0 views
An ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi miliyan ɗaya a  yankin Arewacin Najeriya da nufin yaƙi da sauyin yanayi da kuma kare muhalli.

Kungiyar Environment Concerned Community da Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta zamani da ci gaban al`umma (CITAD) ke jagorantar shirin, wanda aka fara gudanar da shi a ranar 2 ga Satumba, 2026, kuma zai ci gaba har zuwa 1 ga Satumba, 2027.

A wani mataki na tabbatar da gaskiya da kuma bibiyar yadda shirin ke gudana, masu shirya shirin sun ƙaddamar da shafin intanet na www.p1mt.ng, wanda zai bai wa masu shuka bishiya damar aikewa da hoton bishiyar da suka shuka tare da bibiyar kowace bishiya daga lokacin rarraba tsirran bishiya zuwa dasawa, tantancewa da kuma sa ido kan yadda bishiyoyin ke rayuwa.

Ana sa ran masu shuka bishiyoyin za su dasa bishiyoyi, su ɗauki hotunansu sannan su ɗora su a shafin, tare da bayanan wurin da aka dasa bishiyar da kuma nau’in bishiyar.

Da yake magana kan shirin, Daraktan Zartarwa na CITAD, Yunusa Zakari Yau ya ce, yawan hayaƙin iskar gas mai gurɓata muhalli da ake fitarwa a Kano ya sa ya zama wajibi a aiwatar da shirin.

Ya ce, bishiyoyi na da muhimmiyar rawa wajen shanye iskar gas mai gurɓata muhalli da kuma rage illolin sauyin yanayi.

“A yau, dashen bishiyoyi ya zama kamar al’ada, saɓanin shekarun 1960 lokacin da aka dasa bishiyoyi, musamman bishiyar neem, ya kasance wani muhimmin al’ada. Idan babu bishiyoyi, a zahiri muna rasa al’adunmu da kuma tarihinmu,” in ji shi.

Ready to PlayFreedom Radio Dutse • 99.5 FM