“Ana hasashen Luka Modric ne zai lashe kyautar Ballon d’Or”

Alamu na nuni da cewa Luka Modric da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta FIFA, ka iya sake lashe kyautar Ballon d’Or bayan da aka sanya sunansa a cikin jerin ‘yan wasa 30 da ke takarar lashe wannan gagarumar kyauta a bana.

Modric zai fafata da Cristiano Ronaldo na Juventus da Lionel Messi na Barcelona da Mohamed Salah na Liverpool wajen lashe wannan kyauta.

A baya-bayannan ne dai Modric ya doke Ronaldo da Salah wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan FIFA a bikin da ya gudana a birnin London a watan jiya, in da Messi ya gaza samun shiga jerin ‘yan wasa uku da suka yi fafatawar karshe.

Ronaldo da Messi dukkaninsu sun lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar-biyar, amma a halin yanzu kambun na hannun Ronaldo kafin a samu sabon magaji a ranar 3 ga watan Disamba mai zuwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *