Mata na sahun baya wajen amfani da intanet – Maryam

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban Al’ummah wato (CITAD) a Najeriya ta bukaci kafafen yada labarai dasu bada gudumwarsu wajen yada manufar kungiyar ta ganin an samu yawaitar mata masu amfani da internet a tsakanin al’ummar kasar nan.

Jami’ar kula da shirye-shiryen kungiyar Maryam Ado Haruna ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da suka gudanar a yau a cibiyar wanda ya mayar da hankali kan yadda za’a magance matsalolin da yanar gizo ke fuskanta da kuma kokarin ganin mata sun shiga sahun gaba wajen amfani da yanar ta gizo.

Malama Maryam Ado Haruna ta kara da cewa ba karamin koma-baya ne ba, ace maza sun fi mata yawa wajen amfani da Internet adon haka ta bukaci mata dasu fito a dama da su.

Ta kuma ce irin wannan taro ana shirya shine a duk Duniya inda masu ruwa da tsaki kan shiga lamarin don ganin an magance matsalolin da ake fuskanta ta fannin amfani da Internet ga mata.

Wakiliyarmu Fatima Idris Ilyasu ta rawaito cewa, taron shi ne irin sa na farko da cibiyar ta gudanar domim ganin sun wayarwa mata kai don ganin suma ba’a barsu a baya ba. Manufar taron dai shi ne samun daidaito tsakanin maza da mata wajen amfani da Internet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *