An kori Kocin Super Eagles Salisu Yusuf

Hukumar kula da kwallon kafar Najeriya, NFF, ta dakatar da mai horas da ‘yan wasan Super Eagles Salisu Yusuf tsawon shekara daya bayan ta same shi da laifin karbar cin hanci.

Wata sanarwa da mai magana da yawun NFF, Demola Olajire, ya fitar ranar Laraba ta ce an dauki mataki ne bayan sun karbi rahoton kwamitin kula da da’a na hukumar, wanda ya bincika sanna ya gano cewa Salisu Yusuf ya karbi na-goro.

Wani hoton bidiyo da aka nada a asirce ya nuna yadda mai horas da ‘yan wasan Super Eagles ya karbi kudi a hannun wasu mutane yayin tattaunawa kan zaben ‘yan wasan da za su taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Mutanen sun ba wa kociyan kudi ne yayin da suka nuna masa tamkar wakilai ne na wasu ‘yan wasa da ke son a dauke su domin taka rawa a gasar CHAN ta masu taka-leda a cikin gida.

Sai dai Salisu Yusuf, ya shaida cewa ba ya tunanin ya karya dokokin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, wadda ta haramta wa jami’anta karbar na-goro.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *