NBC a Najeriya zata rufe kafafen yada labaran ta ke bi bashi

Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya NBC ta ce, zata rufe gidajen rediyo da talabijin da hukumar ke bin su bashin kudaden sabunta lasisi.

Babban daraktan hukumar Ishaq Modibbo Kawu ya bayyana hakan a yayin ganawa da ‘yan jaridu a birnin Lagos bayan kammala taro da masu ruwa da tsaki.

Alhaji Ishaq Modibbo Kawu ya ce duk wata kafar yada labarai da ta gaza wajen biyan bashin da ake bin ta kafin nan da ranar 15 ga watan Satumba, hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen garkame gidajen kafafen yada labaran.

Ya ce hukumar ta NBC na bin bashin fiye da Naira biliyan 4 da wasu kafafen yada labarai da suka ki biya.

A cewar Alhaji Moddibo a watan Fabrairun bara ne hukumar ta kulla yarjejeniya da masu ruwa da tsaki kan yadda za su biya bashin da ake bin su, amma sai ga shi sun yi watsi da waccan yarjejeniya.

Sai dai da aka nemi da ya bayyana sunayen kafafen yada labaran da suka yi taurin bashin, Babban Daraktan ya kara da cewar bai da ce hukumar ta dauki wannan matakin ba, kasancewar akwai dangantaka mai karfi tsakanin hukumar da kungiyar kafafen yada labarai ta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *