Tawagar ‘Yan kokawar Najeriya sunyi kokari a Algeria

Shugaban hukumar kula da wasan kokuwa na Najeriya, Daniel Igali, ya yabawa ‘yan wasan kokuwar da suka wakilci Najeriya a gasar wasannin motsa jiki na matasa ta nahiyar Afrika, da Algeria ta karbi bakunci na wannan shekara.

Yayin wasannin da aka kammala a karshen makon da ya gabata, wato Asabar, 28 ga watan Yuli, 2018, Najeriya ta lashe lambobin Zinare 3, Azurfa 7 da kuma Tagulla 9 a gasar kokuwa kadai, daga cikin jimillar lambobin yabo 103 da kasar ta lashe yayin wasannin motsa jikin, da ta kammala a matsayi na 5. Lambobin da Najeriya ta lashe a wasanni daban daban da ta fafata a ciki, sun hada da Zinare 29, Azurfa 32 da kuma Tagula 42.

Kasar Masar ce ta lashe gasar wasannin motsa jikin ajin matasa ta bana, bayan lashe jimillar lambobin yabo 199, da suka hada da Zinare 101, Azurfa 55 da kuma Tagulla 43.

Algeria ke biye da Masar da Zinare 71, Azurfa 72 da tagulla 83, jimillar lambobin yabo 226. Tunisia ke a Matsayi na Uku da Zinare 36, Azurfa 46 da tagulla 54, jimillar lambobin yabo 136, sai kuma Morocco ta kasa ta hudu, da jimillar labobi 106, Zinare 29, Azurfa 37 da Tagulla 40.

A shekarar 2010 aka soma wannan gasa ta wasannin motsa jikin Nahjiyar Afrika ajin matasa, wadda take gudana duk bayan shekaru hudu. Gasa ta gaba za ta gudana a shekarar 2022, kuma kasar Lesotho ce za ta karbi bakuncinta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *