An gurfanar da wasu jami’an INEC a gaban Kotu a Najeriya

Hukumar EFCC a Najeriya ta gurfanar da wasu manyan jami’an hukumar zaben kasa mai zaman kanta INEC na jihar Ogun a gaban babbar kotun jihar Legas saboda zargin sama da fadi da kudi kimanin Naira miliyan 179.

EFCC ta gabatar Yemi Akinwomi da Dickson Atiba da kuma Ogunmodedeoladayo a gaban Mai Shariha Sule Hassan na zargin hada baki domin amfana da kudaden da bai halatta a agaresu ba  tare da bin hanyar da ta ba dace ba na karabar kudade.

Wadanda ake zargin dai sun karbi kudaden ne daga Bankuna da dama masu zaman kansu a daf da lokacin da za a fara zaben shekarar 2015. Sai dai dukkanin su sun musanta zargin da ake yi musu.

Daga nan mai Shariah Sule Hassan ya dage cigaba da sauraran shariar har sai ranar 6 ga watan Augusta mai kamawa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *