Hukumar EFCC a Najeriya ta karyata ikirarin da Ayo Fayose yayi

Hukumar dake yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, EFCC ta karyata ikirarin da gwamnan jihar Ekiti mai barin gado yayi kwanakin baya a shafinsa na Tweeter cewa zata dawo da shari’ar da ake wa gwaman jihar ta Ekiti Ayo Fayose.

Hakan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Wilson Uwujaren ya fitar a jya da daddare cewa sanarwar da gwamnan ya fitar na kamashi da za’a yi bayan ya mika milki bai fito daga hukumar ta EFCC ba.

Sanarwar wadda take a @officialEFCC da aka fitar, hukumar ta dawo da zargin shari’ar da ake yi wa gwamnan Ayo Fayose na yin zambar Naira biliyan fiye da dubu guda.

An dai fitar da sanarwar ne bayan awanni da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar kasan sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asbar a jihar ta Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *