Osinbajo ya ziyarci shalkwatar Google

Mataimakin shugaban Nageriya farfesa Yemi Osingbajo ya ziyarci shalkwatar kamfanin Google a Silicon yau Talata a wata ziyara daya kai kasar Amurka.

A yayin ziyarar Mataimakin shugaban kasar ya gana da shugaban kamfanin Google Sundur Pichai wanda ya marabceshi da tawagarsa bisa ziyarar da suka kai shalkwatar kamfanin. Inda ya jagoranci tawagar shuwagannin kamfanin wajen ganawa da farfesa Yemi Osingbajo da sauran jami’an gwamnatin Najeriya.

Mr. Osingbajo ya kuma gana da kamfanonin zuba jari daban-daban, inda ya tattauna da manyan kamfanonin fasaha na kasar Amurkan da manufar bunkasa ayyukan fasaha a kasarnan.

Cikin tawagar matemakin shugaban kasar harda Dr Okey Enelemah da Amb. Dipe Olu da sauran mukarraban Gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *