Za a dauki sabin Yan Sanda a Najeriya – SP Abdu

Shalkwatar rundunar ‘yansanda ta jihar Jigawa ta ayyana ranar 14 ga wannan watan a matsayin ranar da za’a gudanar da jarrabawa kan darussa 6 na makarantar koyon aikin dansanda da aka shirya gudanawar a cibiyoyi 19 na fadin kasarnan.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun rundunar yansandan na jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya sanyawa hannu, yana mai cewa wadanda zasu yi jarrabawar na iya zaunawa a cibiya mafi kusa dasu.

Za dai a fara tantance masu zana jarrabawar da misalin karfe 7 na safe yayinda za’a fara jarrabawar da karfe 10 na safiyar ranar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *