Baiwa Mata Ilimi shine cigaban al’umma – Lai Muhammad

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya Alhaji Lai Muhammad yace ya zama wajibi kasarnan tafi maida hankali kan karatun ‘ya’ya mata, duba da yadda mata ke daukar kaso mai yawa wajen ciyar da al’umma gaba.

Ministan ya bayyana hakan a yayin tattaunawa kan lamuran yada labarai game da ‘ya’ya mata da aka shirya aka kuma gudanar a jihar Zamfara mai taken G4G a takaice, inda yace yara mata nada matukar muhimmanci a cikin al’umma dake bukatar karfafa musu gwiwa musamman a fannin ilmi.

Hukumar kula da hakkokin yara a karkashin ma’aikatar yada labarai da al’adu ta kasar ce dai ta shirya tattaunawar da hadin gwiwar asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, domin tattauna hanyoyin da za’a wayar da kan al’ummar arewacin kasarnan game da ilmin na ‘ya’ya mata.

Tun a bara ne dai asusun tallafawa kananan yara na UNICEF ya kaddamar da shirin na G4G a takaice kashi na 3, wadda ake aiwatarwa a arewacin kasarnan da hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da manufar karfafa gwiwar ‘ya’ya matan domin samun ilmin da zai taimaka musu wajen bunkasa cigaban rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *