An yankewa Gwamnati wutar lantar a Najeriya

Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Enugu dake Najeriya ya yanke wutar gidan gwamnatin Jihar Imo tare da Sakatariyar Jihar saboda bashin naira miliyan dari biyu da yake bi.

Mai magana da yawun kamfanin Emeka Ezah ne ya bayyana hakan ga manema labarai, ya na mai cewa ba san ran su bane maganar ta je kafofin yada labarai, sai dai dan barazanar ruguje ginin kamfanin da gwamnatin jihar Imo tai musu.

Emeka ya kuma ce ana ta kokarin yadda za’a shawo kan matsalar har gwamnatin ta biya kudaden.

A ta bakin Emeka kin biyan kudin wutar da masu ruwa da tsaki ke yi, ka iya haifar da matsaloli tsakanin kamfanin da talakawan gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *