Rasha 2018: Mikel Obi na Najeriya yaji rauni

Tawagar Likitocin kungiyar Najeriya Super Eagles da ke wakiltan Najeriya a gasar cin kofin duniya a Rasha na aiki ba-dare-ba-rana don ganin Mikel Obi ya samu cikakkiyar lafiyar buga wasan da Najeriya za ta yi da Argentina a Talatar nan.

Binciken likitocin ya nuna cewa, dan wasan ya samu rauni a wuyar hannunsa a dai dai lokacin da ake dab da tashi wasan da Najeriya ta casa Iceland da ci 2-0 a ranar jumm’ar da ta gabata.

Koda dai Kocin Super Eagles, Gernot Rohr na kallon runin a matsayin karami wanda kuma ba zai hana Obi buga wasan da Argentina ba.

Rohr ya kuma bukaci ‘yan wasan nasa da su rika dukan kwallo da zaran sun hangi wata kafa a dab da ragar Argentina. Kazalika a cewarsa, wasan na gobe ba zai kasance mai sauki ba, kuma za su yi fafatawar ce da burin samun nasara amma ba canjaras ba kamar yadda wasu ke akalla fata.

Masharhanta kan harkokin wasanni na kallon wasan a matsayin mai zafi kwarai, lura da cewa Argentina na neman nasara ruwa a jallo don tsallakawa matakin gaba, yayin da ita ma  Najeriya za ta yi kokarin samun karin maki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *