‘Yan Wasan Super Eagles sun yi taron gaggawa a Rasha

Tawagar Najeriya Super Eagles dake halartar gasar cin kofin duniya, sun kir wani taron gaggawa a karkashin jagorancin kaftin din su Mikel Obi, inda suka tattauna dangane da yadda za su samu nasara a wasannin da suka sanya a gaba, musamman wasansu da Iceland a ranar Juma’a.

Rashin nasarar da Najeriya ta yi da 0-2 bayan fafatawa da Croatia a wasanta na farko, ya sa tilas sai ‘yan wasan Super Eagles sun samu nasara akan Iceland, don kaucewa fuskantar irin abinda ya faru ga Masar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa baki dayan ‘yan wasan na Super Eagles basu ji dadin tsarin da kocinsu Gernot Rohr ya yi amfani da shi a wasansu na farko ba.

‘Yan wasan, sun kuma bukaci kaftin dinsu Mikel Obi, ya matsawa mai horar da su, da ya kyale kowa ya buga wasan ranar Juma’a a bangare, ko sashin da ya fi kwarewa akai, zalika yayi amfani da masu jefa kwallo 2 a gaba, a maimakon guda 1.

Sai dai a yayinda ‘yan wasan Najeriya, sukai taro na musamman kan kalubalen da suke fuskanta a gasar cin kofin duniya, mai horar da ‘yan wasan Iceland, Helgi Kolviasson, ya ce zasu fafata da ‘yan wasan na Najeriya a ranar Juma’a tamkar suna buga wasan karshe ne na gasar cin kofin duniyar ta bana, lamarin da ke nuna da kawai aiki ja a gaban Super Eagles.

A cewar kocin na Iceland, suna sane da cewar wasansu da Najeriya ba zai zo musu da sauki ba, dan haka, zasu bada dukkan karfin da suke da shi a wasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *