PDP ta goyi bayan karrama MKO Abiola

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce dari bisa dari ta goyi bayan duk wata karrama wa da za a yiwa wanda ake zaton ya lashe zaben shugabancin kasar nan da akayi na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 wato MKO Abiola.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Mista Kola Olgbondiyan ya fitar.

Sai dai jam’iyyar ta ce tayi alla wadai da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duka na yi amfani da bada lambar Yabon domin cimma muradun sa na siyasa a shekarar 2019.

Inda ta ce bayar da wanna lambar yabo wadda ya kamata a ce tun a baya aka bada ita kamar dawo da hannun agogo baya ne kuma ba zai karawa shugaban kasar wani karsashin a harkar siyasa ba.

Haka kuma a lokacin da jam’iyyar ta PDP ke taya iyalan Abiola murnar karrama shi da aka yi da sauran wadanda suka yi shahadar siyasa lokacin zaben 12 ga wan Yunin, jam’iyyar ta bukaci da a tuna mutane irin su Sanata Abrahma Adesanya, da Bagauda Khalto, da kuma Dan Sulaiman sai Raph Obirah Alex Iburu da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *