Lauya Sakataren labaran PDP ya bayyana a gaban kotu

Akalla bayan Sa’o’i 24 bayan sanar da janyewarsa daga kare tsohon Sakataren yada labaran PDP Olisa Metuh a gaban Kotu, Lauyan mai lambar kwarewa ta SAN Mista Emeka Etiaba ya sake bayyana a gaban Kotun a safiyar yau Talata.

Sai dai Olisah Metuh wanda ya yanke jiki ya fadi yayin zaman Kotun na jiya bai bayyana ba a yau, amma Emeke Etiaba ya gabatar da kansa a matsayin Lauyan Metuh.

Mai Shari’a Okon Abang ya ayyana abinda Lauyan Metun ya yi a zaman Kotun na jiya a matsayin rashin da’a da kuma kin bin ka’idojin aiki, bayan da ya fice daga cikin Shari’ar sakamakon dagewa da alkalin ya yi na ci gaba da zaman duk kuwa da faduwar Olisa Metuh.

Daga nan ne ma mai Shari’a Okon Abang y adage zaman kotun zuwa yau Talata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *