Gwamnatin Najeriya zata gina layin Dogo daga Badin zuwa Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kwantiragin Dala biliyan 6 da miliyan 68 da wani kamfanin kasar China don gina layin dogo daga garin Badin zuwa Kaduna, daga cikin aikin layin dogon da ya tashi daga Lagos zuwa Kano.

Wannan jawabi na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar yada labaran ma’aikatar Sufuri Yetunde Sonaike ta bayan jiya a Abuja, tana mai cewa Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar don fara aikin na Badin zuwa Kaduna.

A cewar sanarwar ministan ya shaida cewa aikin zai kammala ne cikin wa’adin shekaru biyu zuwa uku, kuma ma’aikatar za ta samar da kudaden da ake bukata a cikin kasafin kudin bana da na badi.

Layin dogon zai bi ta garin Oshogbo zuwa Ilori zuwa Minna, yayin da wani layi guda daga Oshogbo zai bi ta Ado-Ekiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *