WAEC za ta gudanar da jarabawar GCE zagaye na 2

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun Sakandire ta yammacin Afirka WAEC, ta ce; nan ba da dadewa ba, za ta gudanar da jarabawar GCE zagaye na 2.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Demianus Ojijeogu.

Sanarwar ta ce, za a fara yin rajista a yau Litinin sha hudu ga watan Mayu a kuma kammala a shida ga watan Yuli.

Demianus Ojijieogu, ta cikin sanarwar dai ya ce, daliban da basu samu damar yin rajista ba har aka rufe websites din hukumar sannan su ka dawo daga bisani suka bukaci rubuta jarabawar, idan har sun iya yin rajista awanni ashirin da hudu kafin fara jarabawar za a kyalesu su rubuta, sai dai za su biya naira dubu ashirin da biyar.

Haka zalika sanarwar ta kuma ce, suma wadanda ke da tawaya a jikinsu za su iya yin rajistar jarabawar sai dai wajibi ne su bayyana nau’in nakasa da suke dauke da ita.

Hukumar ta WAEC ta cikin sanarwar dai, ta ce; masu sha’awar rubuta jarabwar za su biya jimillan naira dubu goma sha uku da dari tara da hamsin da kuma wani naira dari biyar lada ga bankuna da sauran masu hannu wajen shirya jarabawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *