Arsenal zata nada sabon koci nan gaba kadan

Arsenal na fatan cewa za ta nada sabon kocin da zai maye gurbin Arsene Wenger kafin a fara gasar cin kofin duniya a wata mai zuwa.

Kocin dan asalin kasar Faransa, wanda saura wasa biyu ya gama aikinsa, zai bar kungiyar ne bayan shafe kusan shekara 22.

Gunners ba su tsayar da ranar nada sabon kocin ba, amma ana sa ran yin hakan kafin fara gasar a Rasha a ranar 14 ga watan Yuni.

Tsohon kocin Barcelona Luis Enrique da Massimiliano Allegri na Juventus ne kan gaba a jerin wadanda ake alakantawa da aikin.

Haka kuma ana rade-radi kan tsohon kyaftin din Arsenal Mikel Arteta da Patrick Vieira a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Wenger.

Baya ga su kuma akwai kocin Monaco Leonardo Jardim da mutumin da ya lashe gasar zakarun Turai sau uku Carlo Ancelotti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *