An dakatar da alkalin wasa dan Najeriya

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta dakatar da alkalin wasa Joseph Ogabor na Najeriya saboda ya yi kokarin karkata sakamako.

CAF ta ce lamarin ya faru ne a wasan da aka buga tsakanin kulob din Plateau United na Najeriya da USM Alger na Aljeriya a gasar cin kofin zakarun Afirka na Confederation Cup ranar 7 ga watan Afrilu a Legas.

Cikin sanarwa CAF, tace Matakin ya biyo bayan bincike da kuma shaidun da jami’an da suka kula da wasan da Afirka ta Kudu suka gabatar, wadanda Ogabor ya tuntuba domin neman su tallafawa kulob din na Najeriya.

An kuma gargadi Plateau United “da su daina bai wa jami’an wasa kyaututtuka wadanda akan iya yi wa kallon wani yunkuri na cin hanci.”

A wani lamarin mai alaka da wannan, sanarwar ta ce “an nemi Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka ta Kudu ta nemi afuwar takwararta ta Najeriya NFF bayan bincike ya nuna cewa babu wata shaida da ta nuna wani jami’in NFF na da hannu a zargin ba da toshiyar baki na dala 30,000”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *