Farashin danyan mai na ci gaba da tashi a kasuwar duniya

Farashin danyan mai na ci gaba da tashi a kasuwar duniya, inda aka sayar da ganga a kan dala saba’in da biyar a kasuwar Brent da ke birnin London.

Rahotanni sun ce ya zuwa karfe takwas da minti goma sha biyar na daren jiya, an sayar da gangan mai guda na Nigeria akan dala saba’in da biyar da santi goma sha shida.

Yayin da a kasuwar West Texas Intermediate da ke Amurka aka sayar da ganga akan dala sittin da takwas da santi talatin da shida.

Masana tattalin arziki dai sun alakanta hau-hawar farashin na danyan mai da ci gaba da samun barazanar tashin hankali a yankunan da ke da arzikin man fetur a duniya.

Sun kuma ce, me yiwuwa kalaman da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi a baya-bayan nan, wanda ya zargi kasar Iran da sharara karya game da ayyukanta na kera makaman Nukiliya, na daga cikin dalilan da suka kara janyo dar-dar a kasuwanni makamashi a duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *