Manchester City ta lashe kofin Premier na 2017/2018

Manchester City ta lashe kofin Premier bayan West Bromwich Albion ta doke Manchester United 0-1 a Old Trafford.

City ta lashe kofin ne da maki 87, inda ta ba abokiyar hamayyarta Manchester United da ke matsayi na biyu tazarar maki 16.

Rodriguez ne ya ci wa West Brom kwallo a ragar United ana minti 73 da wasa.

Kofin Premier na farko ke nan da City ta dauka tun wadanda ta lashe a 2014 da kuma 2012.

Kocin kungiyar Pep Guardiola wanda ya samu nasarori a Barcelona da Bayern Munich ya ce nasarar lashe kofin Premier a Manchester City shi ne mafi girma a rayuwarsa.

Samun nasara a kan Tottenham ci 3-1 a ranar Asabar ne ya taimakawa City lashe Premier a karshen makon nan bayan Man United ta kasa cin West Brom a karawar mako ta 34.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *