Category Archives: Siyasa

An rantsar da mai shari’a Uwani a matsayin shugabar kotun kolin Najeriya

Babban jojin Najeriya mai shari’a walter Onnoghen ya rantsar da mai shari’a Uwani Musa Abba Aji a matsayin shugabar kotun kolin kasar bayan da ta shafe shekaru 14 tana jagorantar kotun daukaka kara. An dai rantsar da ita ne a kotun kolin da ke babban birnin tarayya Abuja. A yayin bikin rantsuwar dai babban jojin…

Read more

An nada sabbin kwamandojin yaki da Boko Haram a Najeriya

Babban hafsan tsaron Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya nada sabbin manyan kwamandoji da ke bada umarnin ga rundunonin hukumar na musamman wadanda ke yaki da mayakan Boko Haram. Wannan nadin dai ya biyo bayan umarnin da Ministan tsaron kasar nan Mansur Dan-Ali ya bayar, na cewa a sauya fasalin rundunar Operation Lafiya Dole don…

Read more

Gwamnati da ‘Yan Kwadago suna cigaba da tattaunawa a Najeriya

Kungiyar kwadago zata ci gaba da ganawa da gwamnantin tarayyar Najeriya kan batun mafi karancin albashi bayan ganawar da suka yi a ranar juma’ar da ta gabata, wanda aka tashi taron ba tare da an cimma wata matsaya ba. Kungiyar kwadagon dai na bukatar gwamnatin kasar ta mika kudurin dokar mafi karancin albashi gaban majalisun…

Read more

Farfesa Osinbajo na halartar taron shugabanin Afrika

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya na kasar Austria don halattar babban taron shugabanin Afrika da na tarayyar Turai da ake yi Vienna ta kasar Austria. Mai Magana da yawon Mataimakin shugaban kasar kan kafafan yada labarai Laolu Akande ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fita a yau a Abuja cewa…

Read more

Rundunar Sojan Najeriya ta bukaci a rufe ofishin Amnesty

Rundunar sojan Najeriya ta yi kira da a rufe offishin kungiyar Amnesty International dake kasar, yayin da take zargin da akwai kwararan hojoji kan kungiyar na kokarin tarwatsa Najeriya. Mai Magana da rudunar Birgediya Janaral Sani Usman Kuka-Sheka ya sanar da hakan, cewa kungiyar na kokarin tarwatsa kasar nan wajen yada kalaman karya na zargin…

Read more

An bude ofishin ‘Yan Fansho a Abuja

Mai dakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bude ofishin kwamitin amintattu na ‘yan fansho da aka sanya masa suna da SINOKI HOUSE dake babban birnin tarayya Abuja. Ginin mai hawan bene 7 hadin gwaiwa ne da kamfanin fansho na Sinoki system International Limited da aka kulla yarjejeniyar shekaru kuma ake tsammanin za’a sami kudaden shiga…

Read more